Yadda Ake Gane Soyayyar Gaskiya
A yau mutane da dama suna fuskantar kalubale wajen bambance tsakanin soyayyar gaskiya da soyayyar karya. Wani zai iya nuna so da kulawa amma zuciyarsa cike take da wata manufa. A wannan rubutu, zamu tattauna alamomin da ke nuna soyayya ta gaskiya, da yadda zaka/raki gane wanda ke son ka/ki da gaske.
1. Kulawa da Hankali
Idan wani na sonki/ka da gaske, zai kula da kai sosai. Zai damu da halinka, lafiyarka, farin cikinka da damuwarka. Kulawarsa ba wai kawai lokacin da yake da bukata ba ne, kullum yana nuna damuwa da kulawa.
2. Girmamawa da Ladabi
Masoyi na gaskiya yana girmama ki/kai. Ba ya raina ki ko ya wulakanta ki a gaban mutane ko a sirrance. Hakan yana nuna cewa yana daukarki da muhimmanci a rayuwarsa.
3. Rashin Boye Sirri
Soyayya ta gaskiya tana buƙatar gaskiya da bude zuciya. Idan masoyinki/ka baya boye sirri ko abubuwan da suka shafe shi/ta, hakan alama ce cewa soyayyar gaskiya ce.
4. Tsare Alkawari
Masoyin gaskiya yana mutunta alkawari. Idan yace zai zo ko yayi abu, sai ya cika. Idan ya kasa, yana bada hakuri da bayani. Rashin cika alkawari sau da yawa na nuna rashin gaskiya ko da’a.
5. Yana Son Ganin Cigaban Ka/Ki
Idan wani na son ka da gaskiya, zai goyi bayan burinka. Zai so ganin ka ci gaba a karatu, aiki ko rayuwa. Ba zai ji kishin cigabanka ba, sai ma ya karfafa ka sosai.
6. Zai Iya Jure Lokacin Wahala
A lokacin da kake cikin matsala ko wahala, masoyin gaskiya ba zai guje ka ba. Zai tsaya tare da kai har sai kun fice daga matsalar. Wannan yana nuna cewa ba dan jin dadi bane kawai yake tare da kai.
7. Bai Neman Lafiya ko Jiki Kawai Ba
Soyayya ta gaskiya ba wai kawai tana neman jiki ko sha’awa ba. Masoyin gaskiya yana so da zuciya, ba wai saboda halittar jiki kawai ba. Idan wanda kake soyayya da shi baya takura ko matsa maka/miki, hakan yana nuna yana daraja soyayyarku.
Kammalawa
Soyayya ta gaskiya ba abu ba ne mai sauki a samu a wannan zamani, amma da lura da wadannan alamomi, zaka iya gane wace soyayya ce ta gaskiya. Kada ka/ki sa zuciya cikin soyayya har sai ka tabbatar da gaskiyar wanda kake soyayya da shi.
Ka taba soyayya ta gaskiya? Ko kina da wasu alamomi da basu zo a nan ba? Rubuta mana a sashin sharhi. Kada ka manta ka raba wannan post din da abokanka don su ma su amfana.